Yadda Harkar Kudi ta Intanet Ta Sa 'Yan Najeriya Tafka Asara
Najeriya a Yau
More Info
Najeriya a Yau
Yadda Harkar Kudi ta Intanet Ta Sa 'Yan Najeriya Tafka Asara
Feb 07, 2023
Halima Djimrao, Muhammad Auwal Sulaiman, Bilkisu Ahmed

Send us a Text Message.

Rashin karfin intanet na wahalar da ’yan Najeriya wajen yin hada-hadar kudi ta intanet.

Yawancin a Najeriya idan mutum zai tura kudi ta intanet yakan kasance cikin fargabar ko kudin ya ki tafiya, ko kuma kudin amma sun ki zuwa wurin wanda aka tura wa.

Shin me ya sa ake yawan samun matsalar tura kudi ta intanet a Najeriya? Shin akwai karfin intanet na amfani domin yin harkar kudi a Najeriya? 

Shirin Najeriya A Yau ya tattauna da ’yan Najeriya da masu sharhi kan al’amarin.