Ko Yaya Mulkin Tinubu Zai Kasance?

Najeriya a Yau

Najeriya a Yau
Ko Yaya Mulkin Tinubu Zai Kasance?
Mar 13, 2023
Halima Djimrao, Muhammad Auwal Sulaiman, Bilkisu Ahmed

Send us Fan Mail

Ganin cewa jam'iyyun adawa sun samu kuri'u sama da miliyan 13 a zaben shugaban kasa da ya gudana ranar Asabar 25 ga watan Fabrairun 2023, shin yaya karfin adawa zai shafi tafiyar gwamnatin zababben shugaban kasar Najeriya, Bola Tinubu?

Shirin Najeriya A Yau ya ji ta bakin wadansu da ba su zabi Tinubu ba a zaben da ya gabata ba, ya kuma ji ta bakin masana kan wannan maudu'i.