Samun abin alheri na sa jama'a jin dadi har murnarsu ta bayyana. Kama daga daurin aure ko suna har ma da cin zabe, ko kammala karatu da sauransu.
Me yasa murna ke rikidewa ta koma tarzoma ko tashin hankali? Mene ne ke janyo yin asara ta dukiya da rayuka a wadansu lokuta yayin murna a Najeriya?
Shirin NAJERIYA A YAU na wannan lokaci ya yi nazarin wannan batun lura da irin abin da ya faru a Jihar Kano bayan zaben Gwamna.