In da ranka, ka sha kallo!
Yanzu haka ‘yan sanda a Jihar Kano suna farautar wata matar kan zargin ta farka cikin wata karamar yarinya ’yar makwabtansu da wata zabgegiyar wuka, bayan da ta dauki yarinyar a hannun iyayenta, da sunan za ta raka ta unguwa.
Ina dalilin wannan danyen aiki da matar ta yi wa wannan karamar yarinya?
Wakilanmu a Kano sun bin diddigi sun samo cikakken bayani daga bakin mahaifin yarinyar kamar yadda za ku ji a cikin shirin Najeriya A Yau.
Ku biyo shirin namu na yau ku ji cikakken bayani.