Yau Litinin 29 ga watan Mayu, za a rantsar da sabon shugaban kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu tare da mataimakinsa Kashim Shettima, kuma a yau din ne suma sababbin gwamnonin jihohi ke yin rantsuwar kama aiki, a cikinsu akwai wadanda aka zaba a karon farko a matsayin Gwamnoni a Arewa kuma a karkashin tutar wata jamâiya ta daban da wadda ta yi mulki a jihohinsu.
Ko wace fata al'ummomin jihohin Arewacin Najeriya 4 ke da ita game da sababbin gwamnonin da suka zaba daga sun yi rantsuwar kama aiki?
Saurari Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci domin jin fata da zaton 'yan Najeriya ga sababbin shugabanninsu.