Dalilin Da Litar Mai Za Ta Iya Haura 700 A Arewa
Najeriya a Yau
More Info
Najeriya a Yau
Dalilin Da Litar Mai Za Ta Iya Haura 700 A Arewa
Jun 30, 2023
Halima Djimrao, Muhammad Auwal Sulaiman, Bilkisu Ahmed

A ranar 30 ga watan Mayu da ya gabata ne kamfanin Man Fetur Na Najeriya (NNPCL) ya bayyana cewa sabon farashin man fetur a Arewacin Najeriya ya zama sama da Naira 530 yayin da a Kudancin kasar ya ke tsakanin 470 zuwa 530, biyo bayan tabbatar da cire tallafin man fetur da sabon shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi a jawabin kama aiki a ranar 29 ga Mayun 2023. 

Mene ne dalilin da ake hasashen litar man fetur za ta iya haura 700 a Arewacin Najeriya, daga watan nan na  Yuli mai zuwa?

Shirin Najeriya A Yau na tafe da bayanan gaskiyar abin da ke faruwa dangane da farashin man fetur din.