Dalilin Da Ya Sa Shinkafa ‘Yar Gida Ke Ƙara Tsada

Najeriya a Yau

Najeriya a Yau
Dalilin Da Ya Sa Shinkafa ‘Yar Gida Ke Ƙara Tsada
Jul 11, 2023
Halima Djimrao, Muhammad Auwal Sulaiman, Bilkisu Ahmed

Send us a text

Har yanzu shinakafa ‘yar gida a Najeriya na ta ƙara tashin gwauron zabi duk da cewa a cikin gida ake sarrafa ta, lamarin da ya sa mutane da dama dake da ƙaramin ƙarfi ba sa iya saya. ‘Yan kasuwa kan shafe tsawon wuni guda ba tare da sun samu cinikin sisi ba.

Ko kun san dalilin da ya sa shinkafa ‘yar gida ke ƙara tsada a Najeriya?

A cikin shirin Najeriya a yau, za ku ji dalilin da ya sa aka gaza samun sauƙin ta, da kuma yadda za a ɗinke bakin zaren.