IPOB Na Kassara Tattalin Arzikin Kasuwanci A Dalilin Dokar Zaman Gida
Najeriya a Yau
More Info
Najeriya a Yau
IPOB Na Kassara Tattalin Arzikin Kasuwanci A Dalilin Dokar Zaman Gida
Jul 25, 2023
Muhammad Auwal Sulaiman, Muslim Muhammad Yusuf, Nana Khadija Ibrahim

Aƙalla kusan Shekaru biyu kenan da ƙungiyar 'yan awaren IPOB ta ƙaƙaba wa mutane zaman gida dole a duk ranakun litinin a yankin kudu maso gabashin Najeriya, a wani mataki na nuna adawa da cigaba da riƙe jagoran su Nnamdi Kanu.

Saidai za a iya cewa lamarin kasuwancin yankin ya soma koma baya sosai, sakamakon yadda ake fargabar ziyartar wannan yanki. Ko da yake su ma wasu mazauna yankin 'yan  ƙabilar Igbo ba su jin dadin tsarin na su.

A cikin Shirin Najeriya a Yau, mun yi nazari kan Ƙalubalen Da 'Yan Kasuwa Ke Fuskanta Saboda Dokar Zaman Gida Ta IPOB.