Yadda Kanawa Ke Gwara Kawunan Su Akan Hotunan Sarakuna

Najeriya a Yau

Najeriya a Yau
Yadda Kanawa Ke Gwara Kawunan Su Akan Hotunan Sarakuna
Aug 01, 2023
Muhammad Auwal Sulaiman, Muslim Muhammad Yusuf, Nana Khadija Ibrahim

Send us a text

Bayyanar hotunan sarki Sanusi na II a ɗakin taro na fadar gwamnatin jihar ya sa ana ta tunanin ko dai gwamnati jihar na shirin mayar wa sarkin sarautar shi ce, kamar yadda wasu ke ta hasashe da zarar sun shiga gwamnati.

Lamarin dai ya yi ta jawo ce-ce-ku-ce, musamman da ake ganin Sanusin na ɗasawa da gwamnatin Jihar. Saidai gwamnatin ta ce ba a saka hoton saboda wata manufa ba sai don tarihi.

A cikin shirin Najeriya a yau, mun duba ainihin abinda ke faruwa gameda maƙala hoton Sanusin a wannan ɗakin taro.