Makomar Jam’iyyar APC Bayan Zaɓen Ganduje
Najeriya a Yau
More Info
Najeriya a Yau
Makomar Jam’iyyar APC Bayan Zaɓen Ganduje
Aug 04, 2023
Muhammad Auwal Sulaiman, Muslim Muhammad Yusuf, Nana Khadija Ibrahim

Jam’iyyar APC mai mulki ta tabbatar da tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje a matsayin shugabanta na ƙasa. Ko da yake lamarin bai zo da mamaki ba, kasancewar an daɗe ana yaɗa wannan jita-jita, wanda wasu ke ganin shi ya sa babu sunansa a cikin ministoci daga jihar.

Ganduje ya maye gurbin tsohon gwamnan Jihar Nassarawa, Abdullahi Adamu wanda ya sauka bisa raɗin kansa, lamarin da ya sa ake ganin an bar yankin Arewa ta tsakiya babu wani jigo a cikin jamiyyar a matakin kasa.

To amma yanzu, mecece makomar jamiyar da inda aka dosa? Shirin Najeriya a Yau ya maida hankali akan hakan