Najeriya a Yau
Me Ya Sa A Ke Naɗa 'Yan Arewa Ministocin Tsaro
Aug 18, 2023
Muhammad Auwal Sulaiman, Muslim Muhammad Yusuf, Nana Khadija Ibrahim
Send us a text
Ƙididdiga ta nuna cewa yawancin ministocin da ake naɗa wa su jagoranci fannin tsaro a mulkin dimokraɗiyya suna fitowa ne daga yankin arewa.
Ƙalubalen tsaro ya fi ƙamari a wannan yanki, abin da ya sa wasu ke ganin hakan wani salo ne da zai sa su maida hankali wajen magance damuwar yankin.
A cikin shirin Najeriya a Yau, mun duba tasirin da nadin 'yan Arewa a matsayin ministocin tsaron gwamnatin Tinubu zai yi tasiri wajen magance matsalolin tsaron yankin.