Wuraren Da Wike Ke Shirin Rushewa A Abuja

Najeriya a Yau

Najeriya a Yau
Wuraren Da Wike Ke Shirin Rushewa A Abuja
Aug 22, 2023
Muhammad Auwal Sulaiman, Muslim Muhammad Yusuf, Nana Khadija Ibrahim

Send us a text

Ana gama rantsar da sabbin ministocin Tinubu, aka hangi sabon ministan Abuja ya nufi ofishin sa inda ya gana da manema labarai kuma ya shaida musu cewa duk wanda ya yi ginin da ya saɓa da tsarin Abuja, zai rushe shi.

Jin wannan sanarwa ta sa hantar wadanda ke zaune a wuraren da ministan ya kira da "Green Areas" a turance. To amma ina ne waɗannan wurare da lamarin zai shafa?

Shirin Najeriya a Yau yana ɗauke da bayanin yadda ministan Abujan ya jefa mazauna garin cikin tunani.