Masu son fara ƙananan sana'o'i kan fuskanci kalubale da dama a lokacin suke yunƙurin ganin sun tsaya da kafafun su, musamman gameda batun rijista da samun haƙƙin mallaka a wasu matakan.
Irin waɗannan matakai ne ke sa mutum ya iya cin gajiyar wani abu idan ya taso da ke buƙatar sai an cika wasu sharuɗɗa. Sai dai ba kasafai ake samun iya cika ƙa'idojin cikin sauki ba.
Shirin Najeriya a yau ya yi nazari akan yadda masu son fara sana'o'i ke shan wahala domin cika matakan da ake buƙata