Jita-jita ta karade kafafen sada zumunta cewa wadansu mata suna zuwa gidajen jama'a da zarar sun yi sallama an amsa sai wanda ya amsa ya sume.
Shin da gaske ne akwai wanda a ka taba yi wa sallama ta sume?
Shirin Najeriya A Yau ya ziyarci jihohin Najeriya hudu domin binciko gaskiyar labarin.