Rasuwar Sheikh Abubakar Giro Argungu sakamakon rashin lafiya a daren shekaranjiya Laraba 6 ga Satumba, ta ruda mutane da dama, a Najeriya da kuma makwabta.
Ko mene ne ya banbanta Sheikh Abubakar Giro Argungu da sauran al'umma?
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci na tafe da bayanai game marigayin, daga bakin makusantansa.