Gwamnatin jihar Borno karkashin jagorancin Farfesa Babagana Umara Zulum ya kaddamar da motocin sufuri a kwaryar birnin jihar, domin rage radadin cire tallafin man fetur din da aka yi a Kasar nan.
Shin ta wadanne hanyoyi za a bi domin kula da wadannan motoci?
Shirin Najeriya A Yau ya ji ta bakin jamaar Borno, ya kuma bi diddigin hanyoyin da gwamnatin za ta bi wurin kula da motocin.