Abin Da Hukuncin Zaben Jihar Kaduna Ke Nufi

Najeriya a Yau

Najeriya a Yau
Abin Da Hukuncin Zaben Jihar Kaduna Ke Nufi
Sep 29, 2023
Muhammad Auwal Sulaiman, Muslim Muhammad Yusuf, Nana Khadija Ibrahim

Send us Fan Mail

Kotun sauraron karar zaben 2023 na gwamnan Jihar Kaduna karkashin jagorancin mai shari’a Victor Oviawe ya ba da umarnin sake gudanar da zabe a rumfunan zabe 24 da ke mazabu bakwai na kananan hukumomi hudu da suka kunshi masu rajista 16,300 a zaman yanke hukunci da ya gudana ta kafar zoom a jiya Alhamis a jihar Kaduna, nan da kasa da kwanaki 90.  

Mene ne wannan hukuncin ke nufi? 


Saurari shirin NAjeriya A Yau na wannan lokaci domin sanin abin da wannan hukuncin ke nufi.