’Yan Bindiga Sun Mayar Da Zamfarawa Bayi A Wurin Hakar Zinare
Najeriya a Yau
More Info
Najeriya a Yau
’Yan Bindiga Sun Mayar Da Zamfarawa Bayi A Wurin Hakar Zinare
Oct 03, 2023
Muhammad Auwal Sulaiman, Muslim Muhammad Yusuf, Nana Khadija Ibrahim

Ta’addancin ’yan bindiga ya dauki sabon salo a Jihar Zamfara, duk da kokarin gwamnati na murkushe su.

Lamarin ya kai ga jama’a na barin gidajensusu, su kwana a dokar daji a yayin da ’yan bindigar suka mamaye wuraren hakar zinare, inda suke tilasta mutane hako musu ma’adinai.

Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci na tafe da karin bayani.