Yadda Gwamnati Ke Shirin Sanya Takunkumi Kan Soshiyal Midiya

Najeriya a Yau

Najeriya a Yau
Yadda Gwamnati Ke Shirin Sanya Takunkumi Kan Soshiyal Midiya
Oct 12, 2023
Muhammad Auwal Sulaiman, Muslim Muhammad Yusuf, Nana Khadija Ibrahim

Send us Fan Mail

Hukumar kula da Kafofin Yaaɗa Labarai ta Najeriya (NBC) na shirin ɓullo da wasu matakai kan masu amfani da shafukan sada zumunta na zamani a wani yunkuri na tsaftace ɓangaren domin hana gurbata tarbiyyar ’yan kasar nan.

Anya zai yi wu a sanya ido yadda ya kamata a kan kafofin sada zumunta yadda ya kamata a Najeriya?

An sha kai ruwa rana da ’yan Najeriya kan wannan kuduri na gwamnati, a shirin Najeriya A Yau mun duba hanyoyi da irin waɗannan matakai za su yi aiki ba tare da matsala ba.