Yadda Barace-Baracen Ƙananan Yara Ke Karuwa A Najeriya
Najeriya a Yau
More Info
Najeriya a Yau
Yadda Barace-Baracen Ƙananan Yara Ke Karuwa A Najeriya
Oct 17, 2023
Muhammad Auwal Sulaiman, Muslim Muhammad Yusuf, Nana Khadija Ibrahim

Rahotanni daga wadansu jihohin Najeriya na bayyana cewa an samu karuwan adadin yara kanana da ke shekarun zuwa makaranta a matsayin mabarata a kan titunan da lungunan manyan unguwanni a sassan kasar nan. 

Shin mene ne ya kawo wannan lamari na adadin yaran da ke bara a tsakanin jamaá a daidai wannan lokaci da ake kurin cigaba, wayewa da sanin kimar bil-Adama? 

Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya dubi wannan batu, ya leka jihar Legas, Kano da kuma jihar Filato da ke arewa ta tsakiyar Najeriya.