A Shekarun baya iyaye kan damka amanar ‘ya’yansu kacokan ga malamai domin karatu da tarbiyya, wannan kuma ba iya malaman addini kadai ba, harda malaman makarantun boko.
Sai dai a ‘yan shekarun nan, iyaye sun samu shakku dangane da hukunta ‘ya’yansu a makaranta, mene ne abin da ya janza har aka samu kai a irin wannan hali?
Shirin Najeriya A Yau na tafe da tattaunawa ta musamman da kwararrun malaman makarnata, masu makaranta da kuma iyayen yaran.