Matsin tattalin arziki da rashin tsaro na daga cikin dalilan da ke turasasawa ‘yan Najeriya tafiya ci-rani kasashen duniya.
Mene ne abin da ya kamata a yi domin kawo karshen wadannan matsalolin?
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya tattauna da masu neman fita, ya kuma bankado gaskiyar abin da ya kamata a yi domin magance yawon ciranin ‘yan Nakeriya a kasashen duniya.