Yawancin mutane na tunanin da zarar mutum na aikin albashi, to za a iya cewa yana shan ƙarfin matsalolinsa.
Saidai da dama daga cikin ma'aikata na cewa albashi ko da nawa ake biyan mutum ba ya iya riƙe shi zuwa ƙarshen wata, sai an yi da ƙyar da cin bashi.
Shirin Najeriya a Yau ya duba yanayin da ma'aikatan albashi ke iya rayuwa tare da albashin su cif-cif har wata ya ƙare