Shin Ko Akwai Lalaci Kan Yadda Wasu Mazan Kan Sakarwa Matan Su Ragamar Gida

Najeriya a Yau

Najeriya a Yau
Shin Ko Akwai Lalaci Kan Yadda Wasu Mazan Kan Sakarwa Matan Su Ragamar Gida
Nov 24, 2023
Muhammad Auwal Sulaiman, Muslim Muhammad Yusuf, Nana Khadija Ibrahim

Send us Fan Mail

Tun dauri a arewacin Naijeriya, Maza aka sani da rike da ragamar gida, ta hanyar fita a nemo abun da za a ciyar da iyali, yayin da mata ke lura da aikace-aikacen gida.

Wasu matan kan yi sana’o’i na gida da niyyar samun kudin kashewa da ba dole sai an tambayi maigida ba.

To a yanzu an shiga yanayin da wasu mazan ke sakarwa mata ragamar gida kacokan. 

Shirin Naijeriya A Yau, ya yi duba ne kan wannan ta’ada ta wasu mazajen, da yadda matan ke fama wajen daukar nauyin gida.