Yadda Ma’aikaciyar Gwamnatin Kano Ta Rasu Saboda Rashin Albashi
Najeriya a Yau
More Info
Najeriya a Yau
Yadda Ma’aikaciyar Gwamnatin Kano Ta Rasu Saboda Rashin Albashi
Dec 12, 2023
Muhammad Auwal Sulaiman, Muslim Muhammad Yusuf, Nana Khadija Ibrahim

Tun bayan da gwamnatin jihar Kano tace ta tantance tare da dawo da wasu ma'aikatan da ta dakatar saboda rashin bin ka'ida, suke ta zura ido domin ganin an biya su hakkokinsu.

Sai dai a yayin da suke jiran, rayuwarsu ta shiga cikin tasku da halin ni 'yasu ta yadda har aka kai ga rasa rai da wasu kalubale da dama.

Shirin Najeriya a Yau ya duba halin da ma'aikatan jihar Kano da aka maida suka shiga saboda rashin biyansu hakkokin nasu.