Shekarar 2023 ta kasance cikin zazzafar siyasa da aka gudanar da babban zaben shugaban kasa da gwamnoni.
Abubuwa da dama sun faru masu daukar hankali da kuma yadda aka samu sauyin salon siyasa a wasu sassan kasar a shekarar dake karewa.
Shirin Najeriya a Yau ya yi nazari kan wasu mahimman abubuwan da suka faru a fagen siyasa a 2023.