Matakan Magance Matsalar Tsaro Kafin 2024 Ta Ƙare

Najeriya a Yau

Najeriya a Yau
Matakan Magance Matsalar Tsaro Kafin 2024 Ta Ƙare
Jan 05, 2024
Muhammad Auwal Sulaiman, Muslim Muhammad Yusuf, Nana Khadija Ibrahim

Send us a text

Tun bayan da gwamnatin tarayya ta sha alwashin dakile matsalar tsaro kafin shekarar 2024 ta kare, jama’a ke ta diga ayar tambayar kan salon da take shirin bi.

Wasu na ganin ba lallai su yarda da kalaman gwamnatin ba. Saidai masana tsaro sun yi hasashen wasu matakai da gwamnatin za ta iya dauka idan har gaske tana son magance matsalar tsaro kafin 2024 ta kare.

Shirin Najeriya a Yau ya duba wasu matakai da suka kamata a bi wajen dakile matsalar tsaro kafin shekarar 2024 ta ƙare.