Makomar Ministar Jinkai Betta Edu Da Shugabar NSIP Halima Shehu

Najeriya a Yau

Najeriya a Yau
Makomar Ministar Jinkai Betta Edu Da Shugabar NSIP Halima Shehu
Jan 09, 2024
Muhammad Auwal Sulaiman, Muslim Muhammad Yusuf, Nana Khadija Ibrahim

Send us a text

Tun bayan dakatar da ministar jin kai ta Najeriya Betta Edu a jiya Litinin 8 ga Janairu da kuma Halima Shehu daga matsayin  shugabar hukumar bada tallafin dogaro da kai ta kasa kwanaki 6 tsakani 'yan Najeriya sun fara bin kwakkwafin wane hali su ke ciki, kuma mene ne abin da ya sa aka dakatar da su? 

Shirin Najeriya A Yau ya binciko cikakken abin da ake zarginsu, ya kuma ji ta bakin masanin shari'a kan makomar wanda ya aikata abin da ake zarginsu da shi.