A ‘yan kwanakin nan hankali ya koma birnin tarayya Abuja ta fannin tsaro.
‘Yan bindiga da masu garkuwa dan neman kudin fansa suna ta farmakar yankunan birnin da ake ganin wuri mafi tsaro a Najeriya.
Shin me ya sa ‘yan bindigar suka karkato da ayyukansu a yankin?
Shirin Najeriya a Yau ya duba abin da ya sa masu garkuwan suka maida hankali kan birin tarayya Abuja.