Hanyoyin Haɗa Kan 'Yan Najeriya Ta Wasan Ƙwallo
Najeriya a Yau
More Info
Najeriya a Yau
Hanyoyin Haɗa Kan 'Yan Najeriya Ta Wasan Ƙwallo
Feb 12, 2024
Muhammad Auwal Sulaiman, Muslim Muhammad Yusuf, Nana Khadija Ibrahim

Send us a Text Message.

Faɗin ƙasa da yawan kabilun da ke Najeriya sun sa zaman 'yan ƙasar uwa ɗaya uba ɗaya masu ƙawazucin juna gagara tun samun ƴancin kai. 

Ko kun san hanyoyin da ya kamata abi domin haɗa kan ƴan ƙasar wuri guda masu so da ƙaunar juna domin ciyar da ƙasar gaba ta hanyar ƙwallon ƙafa? 

Lura da goyon baya da fatan alkhairin da 'yan Najeriya suka nuna wa tawagar ƙwallon ƙafar Najeriya a gasar AFCON, mun dubi hanyoyin da za a bi domin samar da ƴan kasa masu haɗin kai da ƙawazucin juna.