Hanyoyin Samun Karin Kudin Shiga Baya Ga Albashi
Najeriya a Yau
More Info
Najeriya a Yau
Hanyoyin Samun Karin Kudin Shiga Baya Ga Albashi
Feb 22, 2024
Muhammad Auwal Sulaiman, Muslim Muhammad Yusuf, Nana Khadija Ibrahim

Send us a Text Message.

A shekarun baya, idan mutum ya samu aikin albashi har murna ake taya shi, dan ana zaton ya kai tudun mun tsira, amma a ýan shekarun nan, masu daukar albashi na cikin wani hali domin kuwa duk karshen wata wani lokaci na biyan bashin da aka ci a tsakiyar watan, wani lokacin ma sai an ciyo wani bashin a iya biyan wani. 

Ko kun san akwai wadansu hanyoyi halastattu da mai daukar alabshi zai iya samawa kansa mafita a wannan yanayi na tsadar rayuwa da rashin darajar Naira? 

Ku biyo shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci domin jin wadannan halastattun hanyoyi na samun karin kudin shiga.