Ranar Mata Ta Duniya: ‘Hakikanin Abin Da Mata Suke Bukata’
Najeriya a Yau
More Info
Najeriya a Yau
Ranar Mata Ta Duniya: ‘Hakikanin Abin Da Mata Suke Bukata’
Mar 08, 2024
Muhammad Auwal Sulaiman, Muslim Muhammad Yusuf, Nana Khadija Ibrahim

Irin wannan rana ta 8 ga watan Maris Majalisar Dinkin Duniya ta ware a matsayin ranar mata ta duniya domin duba rawar da suke takawa a fannoni daban-daban.

Wasu na ganin mata da dama da ke yiwa junan su hassada ya sa ba a samun ci gaban da ya kamata. yayinda ake ganin ya kamata a rika tallafawa ci gaban mata da kuma habaka tunaninsu.

Majalisar Dinkin Duniya, ta ce  akwai mata kusan miliyan 342 da ke cikin barazanar fadawa  kangin talauci nan da shekarar 2030. Sai dai ta ya za a kaucewa hakan?

Shirin Najeriya a Yau ya yi duba kan wannan rana da kuma yadda za a tallafi matan a fannoni daba-daban.