Makomar Mutanen Da Aka Wanke Daga Zargin Alaƙa Da Boko Haram

Najeriya a Yau

Najeriya a Yau
Makomar Mutanen Da Aka Wanke Daga Zargin Alaƙa Da Boko Haram
Mar 28, 2024
Muhammad Auwal Sulaiman, Muslim Muhammad Yusuf, Nana Khadija Ibrahim

Send us a text

Mutum sama da 300 aka saki ga gwamnatin jihar Borno a satin nan bayan wanke su daga zargin kungiyar Boko Haram.

An dade ana tsare da su tsawon shekaru amma sai yanzu aka gano ba su da hannu. To amma me dokar kasa tace game da irin wannan tuhuma bayan an gano gaskiya?

Shirin Najeriya a Yau ya yi nazari kan halin da aka jefa su da kuma yadda doka za ta yi musu adalci.