Ana cikin matsanancin karancin ruwa a yankuna daban-daban a Najeriya.
Lamarin ya sa a 'yan shekarun mutane ke ta kokarin samar da rijiyoyin burtsatse wato 'Borehole' a turance. Sai dai a cewar masana yawanci yanzu rijiyyoyi na kafewa da kuma haifar da zaizayar kasa.
Shirin Najeriya a Yau ya duba yadda ko haƙa bohol-bohol zai iya haifar da matsala ga muhalli da kuma al'umma a anguwanni?