Abin Da Ya Sa Gwamnonin Arewa Suka Je Amurka Taron Tsaro

Najeriya a Yau

Najeriya a Yau
Abin Da Ya Sa Gwamnonin Arewa Suka Je Amurka Taron Tsaro
Apr 29, 2024
Muhammad Auwal Sulaiman, Muslim Muhammad Yusuf, Nana Khadija Ibrahim

Send us a text

Gwamnonin Arewacin Najeriya da ake fuskantar kalubalen tsaro na kokarin lalubo ko ta wace hanya a samu dabarar dakile matsalar.

Tafiyar  gwamnoni 9 daga arewacin Najeriya zuwa Amurka a kwanan nan domin halartar taron tsaro ya nuna yadda suke kokarin daidaita lamarin har a matakin kasashen ketare.

Saidai lamarin na zuwa ne a lokacin da wasu ke ganin an yi makamancinsa a Najeriya ba tare da halartar wani gwamna daga jihohin da suke fama da matsalar tsaron ba.

Shirin Najeriya a Yau ya duba tasirin da taron zai yi wajen magance matsalar yankunan.