“Tabbas Muna Biyan Ma’aikatan Borno Albashin N7,000, Amma...”

Najeriya a Yau

Najeriya a Yau
“Tabbas Muna Biyan Ma’aikatan Borno Albashin N7,000, Amma...”
May 02, 2024
Muhammad Auwal Sulaiman, Muslim Muhammad Yusuf, Nana Khadija Ibrahim

Send us a text

Shafukan sada zumunta na ta girgiza bayan da wani labari ya bayyana game da yanayin walwalar ma’aikata da albashinsu a jihar Borno.

Ma’aikata da dama sun yi ta yada hoton albashinsu na N7,000; wasu N8,000 ko N13,000 ko N15,000 ga ma’aikatan lafiya.

Shirin Najeriya a Yau ya gano gaskiyar abin da ya sa gwamnatin jihar Borno ke biyan irin wannan albashi da wasu suka ce bai taka kara ya karya ba.