Gwamnatin Zamfara Ta Sa Zare Da Ta Tarayya Kan Yaƙi Da ’Yan Bindiga
Najeriya a Yau
More Info
Najeriya a Yau
Gwamnatin Zamfara Ta Sa Zare Da Ta Tarayya Kan Yaƙi Da ’Yan Bindiga
May 13, 2024

Send us a Text Message.

Takaddama a tsakanin gwamantin Tarayya da ta jihar Zamfara a kan hanyar da ya kamata a bi don kawo karshen matsalar tsaro na neman yin kafar ungulu ga yunkurin kawar da barazanar ’yan bindiga.

Gwamnatin Jihar ta Zamfara dai ta sa kafa ta shure duk wani yunkuri na sasantawa da ‘yan bindiga tana mai cewa ba da ita ba, sannan ta zargi gwamnatin Tarayya da hawa teburin shawarwari da ‘yan fashin daji ba da saninta ba.

Ku biyo mu a Shirin Najeriya a Yau don mu duba abin da ya sa ake samun tankiya game da matsalar tsaro tsakanin gwamnatin tarayya da ta jihar Zamfara.