A baya-bayan nan mazauna manyan biranen Najeriya na ta kokawa game da yadda masu gidajen haya ke neman mai da su saniyar tatsa wajen tsuga kudin haya.
Sai dai masu gidajen na cewa ana fama da tsadar rayuwa kuma kula da irin wadannan gidaje na cin kudi sosai.
Shirin Najeriya a Yau ya yi nazari kan yadda lamarin ke shafar rayuwar mutanen da suke zaune a gidajen haya.