Yadda Za Ku Ceto Yaron Da Ya Kamu Da Jijjiga
Najeriya a Yau
More Info
Najeriya a Yau
Yadda Za Ku Ceto Yaron Da Ya Kamu Da Jijjiga
May 20, 2024
Muhammad Auwal Sulaiman, Muslim Muhammad Yusuf, Nana Khadija Ibrahim

Shin kun taba cin karo da yara masu jijjiga? wani yanayi ne da larurar kwakwalwa ko kasancewar guba a cikin jinni kan haifar wa manya, zazzabi mai tsanani kuma kan haifar wa yara.

Yanayin kan sa yaro ya shiga yanayin sarkewar gabobin jiki da numfashi kamar dai mai farfadiya a wasu lokutan.

Shirin Najeriya a Yau na dauke labarin wata matar da irin hakan ya faru ga 'yarta har ma da shawarwarin masana game da matakin da za ku iya dauka da alamomin da za ku iya gane mutum na cikin wannan yanayi.