Ana ci gaba da bayyana mabanbantan ra’ayoyi tun bayan jawabin shugaba Tinubu kan tsadar rayuwa.
Wasu na ganin kamar bai tabo inda yake musu kaikayi ba, musamman game da batun nan na tallafin man fetur.
Shirin Najeriya a Yau zai yi sharhi kan abin da ya sa ‘yan kasar ba su gamsu da jawaban shugaban ba.