Matasa na ta hankoron a ba su dama domin su jagoranci shugabanci da dora shugabanni na gari.
Sai dai wasu na ta diga ayar tambaya ko matasan za su iya tabuka abin kirki ba tare da sun bayar da kunya ba.
Shirin Najeriya a Yau ya tattauna kan yiwuwar matasan na iya yin abin da ya dace.