Me Ya Sa 'Yan Siyasa Ke Naɗa Tarin Mataimaka A Gwamnati?

Najeriya a Yau

Najeriya a Yau
Me Ya Sa 'Yan Siyasa Ke Naɗa Tarin Mataimaka A Gwamnati?
Aug 26, 2024
Muslim Muhammad Yusuf

Send us a text

Gwamnatoci a matakai daban-daban na ta ikirarin rage kashe kudin gwamnatin ko tsuke bakin aljihu.

Sai dai masu sharhi na gani wasu masu mukaman siyasa ke nada tarin mataimaka wadanda wasu ma ba lallai sun taba ido biyu da su ba.

Shirin Najeriya a Yau zai yi sharhi ne kan rawar da masu taimaka wa ‘yan siyasa da yawa ke taka wa.