Wata Babbar matsala da ambaliyar ruwa ke haifarwa a Najeriya ita ce, yadda dubban mutane ke rasa muhallansu a duk shekara.
Alkalumman hukumar bayar da Agajin gaggawa ta NEMA sun nuna cewa kawo yanzu, ambaliyar ta raba kusan mutum dubu 208,655 da muhallansu a jihohi 28.
Shirin Najeriya a Yau, ya tattauna kan irin matakan da suka kamata a dauka domin kaucewa matsalar da hakan ka iya haifarwa ga al'umma.