Shin Dole Ne Sai An Dauki Tsauraran Matakan Saita Najeriya?

Najeriya a Yau

Najeriya a Yau
Shin Dole Ne Sai An Dauki Tsauraran Matakan Saita Najeriya?
Sep 12, 2024
Muslim Muhammad Yusuf, Ummu Salmah Ibrahim

Send us a text

Duk da kokawa da Yan Najeriya ke ci gaba da yi kan irin manufofin gwamnati da suka ce suna Kara jefa su cikin kangin rayuwa.

Amma, a ko da yaushe Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu Yana kara nanata cewa, tilas ne a dauki tsauraran Matakai na saita tattalin arzikin kasar, idan har ana bukatar Jin dadi a nan gaba.

Shirin Najeriya a Yau zai tattauna ne, kan ko tilas ne sai an dauki tsauraran Matakan, kafin saita tattalin arzikin Najeriya?