“Akwai Yiwuwar Kwata Ambaliyar Borno A Wasu Jihohin”

Najeriya a Yau

Najeriya a Yau
“Akwai Yiwuwar Kwata Ambaliyar Borno A Wasu Jihohin”
Sep 16, 2024
Muslim Muhammad Yusuf

Send us a text

Rahotanni sun ce al’ummomin wasu yankuna a wasu jihohin Najeriya suna zaman ɗar-ɗar bayan da ruwa ya fara mamaye gonaki da gidajensu.

Tun bayan mummunar ambaliyar ruwa a Maiduguri, hukumomi a Najeriya suke kara ankarar da al'ummomin wasu jihohin cewa akwai yiwuwar samun ambaliyar.

Shirin Najeriya a Yau  zai tattauna kan yadda za a dauki matakan kan-da-garki kan yiwuwar ambaliyar.