Matakan Da Wasu Al’ummomi Suke Dauka Don Guje Wa Ambaliyar Ruwa

Najeriya a Yau

Najeriya a Yau
Matakan Da Wasu Al’ummomi Suke Dauka Don Guje Wa Ambaliyar Ruwa
Sep 19, 2024
Muslim Muhammad Yusuf, Ummu Salmah Ibrahim

Send us a text

Wasu al’ummomi a Najeriya sun fara ɗaukar matakan kauce wa asarar da ambaliyar ruwa ka iya haifar musu idan aka buɗe Madatsar Ruwa ta Lagdo da ke Jamhuriyar Kamaru.

A kwanan nan ne dai Hukumar  da ke Kula da Albarkatun Ruwa ta Najeriya ta ce yankunan da ke gaɓar Kogin Binuwai a jihohi 11 na fuskantar barazanar ambaliyar.
Shirin Najeriya a Yau zai yi nazari a kan wadannan matakai da ma hanyoyin magance matsalar gaba ɗaya.