Hakikanin Dalilan Nasarar APC A Zaben Gwamnan Jihar Edo

Najeriya a Yau

Najeriya a Yau
Hakikanin Dalilan Nasarar APC A Zaben Gwamnan Jihar Edo
Sep 24, 2024
Muslim Muhammad Yusuf, Ummu Salmah Ibrahim

Send us a text

Duk da kokawa da ’yan Najeriya suke ci gaba da yi game da wahalhalun da suke sha wadanda suka zargi manufofin Gwamnatin Tarayya ta APC da haddasa musu, wasu sun ce bas u yi mamaki ba da al’ummar Jihar Edo suka zabi jam’iyyar.

Sai dai kuma abin tambaya shi ne: mene ne hakikanin dalilinsu na yin haka?

Shirin Najeriya A Yau zai yi binciken kwakwaf a k kan ikirarain shugabannin APC cewa amincewa da salon mulkin jam’iyyar ne ya sa al’ummar Jihar Edo suka zabe ta.