Yadda Rusau Ke Jefa Rayuwar 'Yan Najeriya Cikin Kunci

Najeriya a Yau

Najeriya a Yau
Yadda Rusau Ke Jefa Rayuwar 'Yan Najeriya Cikin Kunci
Dec 09, 2021
Halima Djimrao, Muhammad Auwal Sulaiman, Bilkisu Ahmed

Send us a text

Duk lokacin da hukumomin tsara taswirar  biranen Najeriya suka tashi jama'a daga inda suke gudanar da harkokin rayuwarsu don gudanar ayyukansu, lamarin na zuwar wa wadanda abun ya shafa da firgici da gigita. 

Wasu mazauna unguwannin da aka umarce su da su yi kaura wani lokacin sukan yi watsi da umarnin hukumar har sai ya kai wa'adin da za a yi amfani da katapila don rushe duk wasu gine-gine da shaguna kafin su tashi daga yankin. 

Wasu da abin yake shafa na ganin hukumomin na zaluntar masu karamin karfi ne kawai.

Shin hukumomin na sanar da jama'ar da lamarin ya shafa kafin a rushe kadarorinsu?

Wasu sun ce, ana yi masu alkawari bayan rushe gidajensu da shagunansu, shin ana cika wadannan alkawurra?