Yadda Karin Harajin 2022 Zai Shafi Rayuwar ’Yan Najeriya

Najeriya a Yau

Najeriya a Yau
Yadda Karin Harajin 2022 Zai Shafi Rayuwar ’Yan Najeriya
Dec 16, 2021
Halima Djimrao, Muhammad Auwal Sulaiman, Bilkisu Ahmed

Send us Fan Mail

’Yan Najeriya na ta yi wa kalaman Ministar Kudin kasar fassara iri-iri bayan ta sanar da yiwuwar karin harajin da gwamnatin kasar ke karba daga hannunsu a shekar 2022 mai kamawa. 

Shin kun kun san ta hanyoyin da wannan karin harajin zai shafi rayuwarku kai-tasaye kuwa?
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya fayyace ma’anar kalaman ministar, sannan ya zakulo hanyoyin da karin harajin zai taimaki tattalin arzikin kasar da kuma yadda zai shafi rayuwar ’yan kasar kai-tsaye.

A yi sauraro lafiya.