’Yan Najeriya da dama na mamakin yadda mutanen da suke gani a matsayin manyan masu laifi ke kubuta idan an kai su gaban kotu.
Sau tari ana murnar an kama mai laifi, amma ana zuwa kotu sai yanke hukunci ya gagara a cikin lokaci; Wani lokaci kuma bayan dan lokaci da yanke mishi hukunci, sai a ga ya dawo cikin al’umma yana harkokinsa.
Ina gizo ke saka, sannan me ya sa mutane debe kauna daga cin nasara a kotunan Najeriya?